Da Dumi dumi kotu ta ce a saki Ndume.
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin Sanata Ali Ndume, wanda aka bayar da umarnin a ranar Litinin a ci gaba da tsare shi a Kuje Correctional Center, Abuja saboda rashin gabatar da tsohon Shugaban, rusasshiyar kungiyar gyara fensho (PRTT), Abdulrashed Maina, ga wanda ya ya tsaya lamuni.
Ndume, wanda ke wakiltar gundumar sanatan Borno ta Kudu, ya kasance a tsare a gidan yari bayan kotu ta gano cewa Maina ya tsallake belin sa.
A hukuncin da ta yanke a ranar Litinin Justice Okon Abang ya ba da bukatar belin har sai an daukaka kara, wanda Maina ya shigar.
Mai shari’a Abang ya ce yana amfani da karfin ikon kotun ne wajen nuna goyon baya ga Ndume bisa la’akari da kyawawan halayensa a yayin shari’ar Maina, wanda ake tuhuma kan zargin badakalar kimanin N2billion.
Cikakkun bayanai jim kadan…

