Labarai

Da Dumi Dumi ‘yan bindiga sun kashe mutun Sha uku a Maradun Dake Jihar zamfara.

Wasu daliban da ke karatu a wata makarantar sakandare a garin Damaga, da ke karamar hukumar Maradun, ta Jihar Zamfara, sun tsere a ranar Laraba lokacin da wasu ‘yan bindiga suka far musu.

Mazauna garin sun ce wasu mutane da dama da ba a san ko su wanene ba sun zo kan babura inda suka bude wuta ba tare da bata lokaci ba.

Akalla mutane 13 aka ba da rahoton sun mutu a harin.

Yan ta’addan Sun isa garin ne da misalin karfe 1 na rana suka fara harbin mutane. Dalibai suna daukar darasi a Makarantar Sakandare a Duk da Daliban da suka ga masu aikata laifin, sai suka fita da ajujuwan suka shiga Gudu.

Wani magidanci mai suna Musa Damaga ya shaida wa majiyarmu cewa, “A yanzu da nake magana da ku, gawarwakin wadanda abin ya rutsa da su kuma mun kammala shirye-shiryen binne su.”

Lokacin da aka tuntube shi, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar, SP Muhammad Shehu, kawai ya ce: “yanzu Bani dan lokaci zan dawo gare ku.”

Zamfara na daya daga cikin jihohin da ‘yan fashi suka mayar da rayuwa muutane Cikin hadari.

Cikin damuwa da yawan hare-hare, Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana jihar a matsayin yankin da Jirgin sama bazai tashi ba sannan ya kuma haramta ayyukan hakar ma’adanai a jihar.

Ya kuma ba da umarnin tura karin dakaru 6000 a cikin jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button