Labarai

Da dumi’dumi: An sace dalibai mata a Jami’ar Dutsin-Ma Dake Jihar katsina.

Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka yi awon gaba da wasu dalibai mata a jami’ar tarayya ta Dutsin-Ma, FUDMA, da ke jihar Katsina, inda ‘yan sanda suka tabbatar da kama daya da ake zargi da hannu a lamarin.

An ce an yi garkuwa da mutanen ne a gidansu da ke bayan makarantar Mariamoh Ajiri Memorial International, daura da hanyar Tsaskiya.

Wani ganau ya ce an sace daliban ne da sanyin safiyar jiya da misalin karfe 2:30 na safe.

‘Yan ta’addan sun mamaye rukunin gidajen daliban da ke bayan makarantar Mariamoh Ajiri International School da sanyin safiyar yau, lamarin da ya sa ‘yan bindigar suka yi awon gaba da dalibai mata biyar na Jami’ar,” inji shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Abubakar Sadiq, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho.

Ya bayyana cewa an kama wani mutum da ake zargi da hannu a lamarin, inda ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike da nufin kubutar da wadanda aka sace daga hannun ‘yan fashin.

“Eh, gaskiya ne lamarin ya faru amma mun riga mun kama mutum daya da ake zargi da hannu a lamarin kuma muna kan binciken lamarin don gano abubuwan da ke tattare da shi don Allah,” in ji Aliyu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button