Labarai

Da dumi’dumi: Gas na girki ya yi tashin gauron zabbbi a wasu sassan Nageriya a na sayarda 12.kg daga N11,500 zuwa N14,000.

Ana kara nuna damuwa kan tashin farashin iskar gas din dafa abinci, domin a yanzu ana sayar da kilo guda tsakanin Naira 1,000 zuwa Naira 1,200 a sassan kasar nan, kamar yadda binciken Daily Trust ya nuna.

Akwai kuma fargabar cewa farashin na iya kara tashi saboda karancin kayan, wanda ‘yan kasuwa ke dangantawa da kawo cikas.

Binciken da ya gudanar a fadin Jihar Legas a jiya ya nuna cewa, yayin da ake sayar da kilo 12.5 na iskar gas a kan Naira 12,000 a wasu gidajen sayar da kayayyaki, an kuma sayar da kilo guda kan Naira 1,150 da Naira 1,200 a wajen Legas kamar Mowe, Ibafo da Magboro, daga cikin su. wasu kuma a kan hanyar Legas zuwa Ibadan a jihar Ogun.

Binciken mu na yau Kuma da ya guda a Arewacin Nageriya na cewa an sayar da 12.5kg ba gas din tsakanin 10,500 -11,500 Zuwa 12,000 a jihar Kano.

A Abuja kuwa ana sayar da 12.kgs kan 11,500 a jihar Nasarawa 9,700 Zuwa 11,500.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button