Da dumi’dumi: Gwamna El rufa’i Ya kafa Kwamitin mika Mulki ga Sanata Uba sani.

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana wani kundin tsarin mulkin kwamitin mika mulki na shekarar 2023, wanda ya kunshi zababbun gwamnatin El-Rufai mai barin gado da Sanata Uba Sani, zababben gwamna Mai zuwa.
A wata sanarwa da gidan Sir Kashim Ibrahim ya fitar ta bayyana cewa kwamitin mai mutum 65 zai shirya taswirar aiwatar da shirin SUSTAIN na gwamnati mai jiran gado wanda ke da tsarin tafiyar da gwamnati don ci gaba da ci gaban da aka samu a jihar tun daga shekarar 2015.
Kwamitin zai kuma shirya bukukuwan shigar sabuwar gwamnati.
Kwamitin mika mulki zai kasance karkashin sakataren gwamnatin jiha Balarabe Abbas Lawal wanda shi ne shugaban kwamitin mika mulki a shekarar 2015 kuma mataimakin shugaba a shekarar 2019.
Nuhu Isyaku Buzun, babban sakataren majalisar zartarwa da harkokin siyasa, zai kasance sakataren kwamitin, wanda nan ba da jimawa ba za a kaddamar da shi.
Sanata Uba sani shine ya lashe zaben Gwamnan jihar Kaduna a zaben Daya gudana.
