Dangote zai tallafa don sake tsugunar da ‘yan Najeriya da aka kwashe daga Sudan

Kwamitin amintattu na gidauniyar Aliko Dangote ta kuduri aniyar bada gudummuwa sosai wajen kwashewa da sake tsugunar da dubban ‘yan Najeriya da suka makale a Sudan.
MD/Shugaban Gidauniyar Aliko Dangote (ADF), Zouera Youssoufou, ta tuntubi mahukuntan Air Peace da Gwamnatin Tarayya don nuna shirin Gidauniyar na tallafawa ‘yan Najeriya da suka makale.
Ta ce: ” Gidauniyar za ta hada kai da Gwamnatin Tarayya da kuma Air Peace wajen tabbatar da zirga-zirgar ‘yan Najeriya da suka makale ba tare da wata matsala ba tare da samar da kayan aiki da tallafi ga wadanda aka kwashe, don sa su samu kwanciyar hankali idan sun dawo Najeriya.”
Gidauniyar ta ci gaba da bayyana cewa, ADF ta fahimci kalubalen da gwamnatin tarayya da kuma Air Peace ke da shi a cikin wannan aiki, kuma ta tuntubi hukumomin gwamnatin tarayya da abin ya shafa, masu ruwa da tsaki wajen ba da agajin bala’o’i, “… yana nuna sha’awarmu ta hada kai da su don tabbatar da cewa dukkan ‘yan Najeriya wadanda suka makale a Sudan an dawo da su gida lafiya.”
Idan za a iya tunawa gidauniyar Aliko Dangote ta tallafa wa gwamnatin Najeriya da tallafin kayan aiki ga ma’aikatan kiwon lafiya na sa kai na Najeriya da suka tallafa wa kokarin dakile cutar Ebola a kasashen Laberiya da Saliyo bayan dawowarsu kasar a shekarar 2015.
Har ila yau, a lokacin barkewar cutar Covid-19 ta kwanan nan, ADF ta tallafa wa dawowar ‘yan Najeriya daga Indiya da Dubai a lokacin barkewar cutar tare da jirage na musamman na haya da gwajin Covid da keɓewa lokacin da suka dawo Najeriya.
Tun daga shekarar 2011, ADF ta tallafa wa ‘yan gudun hijira dubbai a Yobe, Borno, Adamawa, da Abuja tare da kashe sama da naira biliyan 25 wajen samar da abinci, matsuguni, da ayyukan kiwon lafiya.
A halin da ake ciki, wata sanarwar hadin gwiwa da ta fito daga ma’aikatar harkokin wajen kasar da ma’aikatar jin kai, da kula da bala’o’i, da ci gaban jama’a ta tarayya, ta bayyana cewa rukunin farko na bas guda 13 dauke da mutane dari shida da talatin da bakwai (637) sun isa iyaka lafiya a Aswan, Misira.

