Duk Wanda Yake Da Bindiga Kowacce Iri Ce Ya Mikata Ga Hukumar ‘Yan Sanda~ Rundunar ‘Yan Sanda.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja ta bukakaci duk wanda ya mallaki Bindiga ya mikata ga Hukumar ‘Yan Sanda Ta kusa dashi, ko kuma ya kai ta Hedikwatar Rundunar ta Jihar dake Dutsen Kuran Kura a Minna babban birnin Jihar.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Adamu Usman, ne ya sanar da hakan, yace hakan Umarnin Shugaban ‘Yan Sanda ne Na Kasa a Kokarin ta na Tabbatar da tsaro a Fadin Kasar Nan.
Usman yace kowacce Irin Bindiga ce ka kaita ga Hukuma, koda kuwa bindigar Kirar gidace ( Harba ruga).
Ya kara da cewa Duk wanda bai maida Bindigar saba daga yanzu zuwa ranar 30 ga wannan watan na Satumba, Idan an kamashi zai fuskanci Shara’a a gaban Kuliya Inji Shi.
Idan dan baku manta ba, tun watanni biyu da suka gabata ne, Shugaban ‘Yan Sandan Kasar Nan IGP. Adamu Abubakar ya sanarda hakan a Jihar Kebbi, Inda yace duk wanda ya mallaki Bindiga ya kaita ga hukumar ‘Yan Sanda na Kusa dashi a kokarin Hukumar na dakile Matsalar tsaro da ta Addabi Arewacin Kasar Nan.
