Labarai

Ga Mahimman Abubuwan da Yakamata Ku sani Game da Sanata Uba sani.

An haifi Sanata Malam Uba Sani a ranar talatin da ‘daya 31 ga Disamba na shekarar alif, 1970, a karamar hukumar Zariya ta jihar Kaduna.

Injiniya ne ta hanyar horaswa, ya yi digirin digirgir a fannin kudi daga Jami’ar Jihar Calabar da kuma Difloma a fannin harkokin kasuwanci a Jami’ar Abuja.

Sanata Uba Sani ya yi zanga-zangar nuna adawa da mulkin soja a Najeriya, inda ya shiga sahun jarumai da kishin kasa, ya yi amfani da kungiyarsa da fasahar sadarwarsa wajen samar da dabara Mai tushe ga yunkurin tabbatar da dimokuradiyya a Arewacin Najeriya. Ya kuma yi amfani da kungiyarsa ta farar hula mai suna (Movement for Freedom and Justice) wajen fafutukar kare hakkin marasa galihu tare da ba su damar samun adalci da ‘yanci ba tare da wata matsala ba Ya samu nasarar rike mukaman mataimakin shugaban kungiyar yakin neman zabe ta kasa (CD) da mataimakin shugaban kwamitin hadin gwiwa na kasa (JACON) karkashin jagorancin Cif Gani Fawehinmi, SAN.

FANNIN SIYASA.

SANATA UBA SANI ya shiga fagen siyasa ne bayan dawowar dimokuradiyya a Najeriya a shekara ta Alif 1999, kuma ya goyi bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar People’s Democratic Party, (PDP) Cif Olusegun Obasanjo bayan lashe zaben matakin shugaban kasa na Obasonjo an nada Uba Sani mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin jama’a. Ya kuma yi aiki a Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA) kan wasu ayyuka na ba da shawara ga Ministan Babban Birnin Tarayya na Lokacin Malam Nasir Ahmad El-Rufai da ma’aikatar gidaje da ayyuka ta Jihar Kaduna. A shekarar 2011 Uba Sani ya tsaya takarar neman kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya a jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) amma yayi rashin nasara a zaben fidda gwani, kuma a shekarar 2015 gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad el-Rufai ya nada shi a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin siyasa da kuma tsakanin gwamnati. Sai dai a shekarar 2019, Uba Sani ya nuna sha’awarsa kuma ya sake tsayawa takarar neman kujerar sanatan Kaduna ta tsakiya a karo na biyu a karkashin jam’iyyar APC mai mulki, kuma an zabe shi a matsayin Sanata a lokacin babban zaben Najeriya na watan Fabrairu 2019.

Uba Sani ya kafa gidauniya Mai suna Uba Sani Foundation a shekara ta 2018. Manufar gidauniyar ita ce tabbatar da samar da ingantacciyar kiwon lafiya, ilimi da inganta rayuwar marasa galihu a Najeriya. Gidauniyar tana amfani da albarkatu da ƙwarewa domin ba da taimako ga marasa galihu a fannin Ilimi da Kiwon lafiya da samun Ƙwarewar Sana’a da Ƙarfafawa.

Ana kuma kallon wakilcin na sanata Uba Sani a majalisar dattijan Nageriya a matsayin wani babban ci gaba ga al’umma musamman a kaunarsa ga bil’adama, a matsayinsa na mai fafutukar kare hakkin bil’adama da dimokaradiyya, dan kasuwa kuma mai taimakon jama’a. Yunkurin da ya ke yi na taimakon jama’a ya sa jama’a da dama a jihar Kaduna da ma wasu ‘yan Nijeriya da dama a fadin kasar nan ke yabawa a gare shi bisa kokari

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button