Halin Mutum Jarinsa: Kyawun hali kamar kyakkyawar sutura yake, domin ba’ajin kunyar Shiga jama’a dashi Yusha’u Mazadu Mutum ne na Mutane


Yusha’u Mazadu: Wani Mutumin kirki ne mai taimakawa jama’a wanda a ko da yaushe muna Alfahari dashi a cikin garin Jos.
Wannan bawan Allah da kuke gani sunansa Yusha’u Mazadu, mazaunin cikin garin Jos babban birnin jihar Filato.
Ya kasance mutum ne Jajirtace, haziki kuma Adali.
Mutum ne wanda yasan ya kamata, sannan ya yi fice afagen kyautatawa Al’ummar da yake tare da su.
Sannan yana daya daga cikin shugabbanin da muke alfahari da su a cikin garin Jos, saboda tausayinsa ga Al’ummah mussaman ma marasa karfi.
Da wannan nake masa Addu’a, Ubangiji Allah ya Albarkaci rayuwarsa da rayuwar Zuri’arsa baki daya, Allah ya biya masa bukatunsa duniya da lahira, Allah ya raba shi da sharrin masu sharri Ya sada shi da masoya na kwarai.
UBANGIJI ALLAH YASA YA GAMA DA DUNIYA LAFIYA🙏
Daga Yusuf Namaska










