Tsaro

Hanyoyi mara sa kyau na kawo mana cikas ga yaki da ‘uan ta’adda a yankin Arewa Maso Gabas, Cewar shugaban Hafsohin Tsaro, Lucky Irabor

Babban hafsan hafsoshin tsaro, Laftanar Janar Lucky Irabor ya ce rashin kyakkyawar hanyar a jihar Borno ya taimaka ga rashin kawo karshen rikicin Boko Haram a yankin.

Janar Irabor ya jagoranci shugabannin hafsoshin ne zuwa Maiduguri, jihar Borno a ranar Lahadi, a matsayin ziyarar aiki ta farko, na Operation Lafiya Dole, tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya nada su.

Yayin da yake tsokaci kan halin da ake ciki a yankin, ya ce har sai an samu isassun tanadi, zai yi wuya a samu nasarar da ake bukata.

“Tantance hanyoyin shine batun kuma wannan ba aikin Operation Lafiya Dole bane. Ba za a iya samun shugabanci na gari ba tare da kyakkyawar hanyoyin ba ”in ji shi.

Babban hafsan tsaron wanda ya lissafa wuraren da hanyoyin zasu taimaka wajen gurfanar da rikicin ya ce sojoji zasu yi abin da ya kamata amma dole masu ruwa da tsaki su yi abin da ya dace don tabbatar da samar da kayan yau da kullun don samar da kafa mai karfi a cikin aikin.

Wadanda ke karkashin jagorancin shugaban hafsan tsaro Janar Lucky Irabor sun hada da shugaban hafsan sojan kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, shugaban hafsan sojin sama, Air Vice Marshal Isiaka Amao da shugaban hafsan sojin ruwa, Rear Admiral Auwal Gambo da sauran manyan hafsoshin tsaro da sauransu.

Manyan hafsoshin da a halin yanzu suna cikin samun bayanin aiki a babban hedikwatar rundunar da ke Maimalari, Maiduguri ana sa ran za su ziyarci gwamnan jihar Borno Babagana Zulum da kuma Shehun Borno Abubakar Garbai Elkanemi.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button