Hukumar EFCC Tayi Nasarar Kama Wasu matasa Guda Tara a Jihar Neja.
Ofishin hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati da zagon Kasa ta (EFCC) ta kama wasu mutane guda tara da ake zargi da Sata ta intanet a Minna fadar gwamnatin Jihar Neja.
Jami’an hukumar ne suka kamo wadanda ake zargin a daki mai lamba 202, Seftec otels, dake bayan gudan man NNPC dake Minna, jihar Neja, saboda zarginsu da hannu a zamba cikin Cikin Aminci da sauran laifukan da suka shafi kafafan Sadarwa.
Wadanda ake zargin sune: Ohanuka. O. Samuel, mai shekaru 26; Adebayo Adeyinka Samuel, mai 26; Omoh Simeon, mai 25; Igah Abumere, mai 28 da Ajobo Lahadi, mai 26.
Sauran sune Abdukadir Musbau, mai 20; Iredia Johnson mai 29, Aliyu Abdulazeez, mai 25, da Adebisi Temitope, mai 27.
Abubuwan da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da, Mota kirar Toyota Venza guda daya da lambar rajista, kwamfyutocin tafi-da-gidanka da wayoyi na zamani a Tare dasu.
Za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu da zaran an kammala bincike Inji Hukumar.
Ahmed T. Adam Bagas


