Labarai

Ku janye Yajin Aiki domin Zamu sayo kayan Abinci mu sayarwa da talakawan jihar Kano a farashin Mai rahusa ~Cewar Gwamna Abba Gida-Gida.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da ta dakatar da shirinta na gudanar da zanga-zanga a fadin kasar, yayin da gwamnatoci a matakai daban-daban ke kokarin ganin an samar da hanyoyin rage radadin da ake fama da shi a sakamakon karin man fetur.

Gwamnan jihar ya bayyana haka ne a yayin wani taron tattaunawa na majagaba tare da mambobin kwamitin sake wayar da kan al’umma (CRC) daga kananan hukumomi 44 da aka gudanar a gidan gwamnati na Africa House.

Wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar a daren ranar Talata, ta ruwaito Gwamnan ya yi kakkausar suka ga shugabannin Kwadago da su yi hakuri saboda ana kokarin ganin an magance matsalolin.

Gwamna Yusuf ya ce a jihar akwai tsare-tsare da gwamnatin jihar Kano ta yi na fitar da matakan da za su dakile tasirin.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Da niyyar samar da matakan dakile illolin cire tallafin, gwamnatin jihar Kano na shirin sayen hatsi daga gwamnatin tarayya da kuma sayar wa al’ummar jihar a kananan hukumomi 44 a kan farashi mai sauki.

“Alh Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatin jihar ta damu da matsalolin da jama’a ke fuskanta sakamakon tsadar sufuri da kayan abinci da tallafin da aka samu ya yi alkawarin samar da karin hanyoyin da za a rage wahalhalu.

“Gwamnan ya kara da cewa ana shirin dawo da motocin Kanawa kan tituna domin daukar Al’umma a sufuri a jihar domin taimakawa dalibai, mata da sauran nau’o’in mabukata kyauta.

“A kan kudirin yajin aikin da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ke yi a duk fadin kasar nan gobe, Gwamnan ya yi kira da kakkausar murya ga shugabannin kungiyar da su yi hakuri su dakatar da yajin aikin da aka shirya gudanarwa a daidai lokacin da gwamnatoci a dukkan matakai ke bakin kokarinsu wajen ganin an samar da hanyoyin rage radadin da ake fama da shi. sakamakon hawan mai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button