Ku Sani fa Haryanzu Nageriya itace Kasa Mafi Rahusar litar man fetir a duk Afrika ~Lai Mohammed
A ranar Litinin din da ta gabata ne Gwamnatin Tarayya ta ce duk da karin farashin da aka yi a kan litar man fetir zuwa N162 kowace lita, haryanzu Nageriya itace Kasa mafi sauki da rahusar Farashin litar man fetir cikin kasashen Afirka. Alh Lai Mohammed ne ya bayyana Haka a wani taro a Abuja a taron Daya samu halartar Ministan Wutar Lantarki, Sale Mamman; da Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva. Ministan yace yanzu a Nageriya litar man fetir -N162 Kacal ake saidawa misali ga Farashin wasu kasashen dake Afrika kamar Haka..
Ghana -N332 kowace lita; Benin -N359 kowace lita; Togo – N300 kowace lita; Niger – N346 kowace lita; Chadi -N366 kowace lita; Kamaru -N449 kowace lita; Burkina Faso -N433 kowace lita; Mali -N476 kowace lita; Laberiya – N257 kowace lita; Saliyo -N281 kowace lita; Guinea -N363 kowace lita; da Senegal – N549 a kowace lita. “A wajen karamin yankin, ana sayar da man akan N211 kowace lita a Masar da N168 kowace lita a Saudi Arabiya.”
Amma duk da cire tallafin farashin mai a Najeriya haryanzu ya kasance Mafi arha a Afirka.Lai Mohammed ya kara da cewa Kuma fa a Haka mun samu ragin kashi 60 daga cikin kudaden shigar kasar, to Maganar Gaskiya gwamnatinmu yanzu ba za ta iya sake cigaba da biyan tallafin man fetir ba, Ya kara da cewa tallafin man fetur kadai ya ci N10.413trn tsakanin 2006 da 2019.

