Kungiyoyi

Kungiyar Matasan Arewa Ta Bada Hakuri Kan Barazanan Datayiwa Inyamurai Cewa Su Fice Daga Arewa A Shekarar 2017.

Shugaban kungiyar matasan Arewa ta AYCF, Shattima Yarima ya bayyana cewa suna baiwa Inyamurai hakuri kan barazanar da suka musu ta cewa su fice daga Arewar a shekarar 2017.

Ya bayyana hakane yayin da ya kaiwa shugaban kungiyar, MASSOB, Ralph Uwazuruike ziyara a birnin Owerri jiya, Juma’a.

Ya bayyana cewa a wancan lokacin suna kokarin ganin sun yaki gurbatattun shuwagabannin Inyamurai ne amma a yanzu yana so ya sanar da Duniya cewa, bangarorin biyu a hade suke sannan kuma zasu kare muradun Inyamurai a Arewa.

Shima ta bangaren sa, Ralph ya bayyana cewa ba zasu bari a taba ‘yan Arewa a jihar ta Imo ba.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button