Tsaro

Maganganun Trump Sun Ƙara Ƙarfafa Masu Ƙiyayya da Tashe-Tashe a Najeriya – SGF Akume

Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), George Akume, ya bayyana cewa kalaman Shugaban Amurka, Donald Trump, game da tsaro da batun “Christian genocide” a Najeriya sun ba wa kungiyoyin ta’addanci ƙarfin guiwa, suna ganin duniya na goyon bayan labaran da suke fakewa da su.

Akume, yayin taron manema labarai a Abuja, ya ce:

Kungiyoyin Boko Haram/ISWAP da barayin daji suna ƙoƙarin fakewa da bayanan Amurka domin su kai sabbin hare-hare.

Trump ya zargi Najeriya da yin shiru kan hare-haren da ake kaiwa Kiristoci — zargi da Akume yace yana ɓata gaskiya kuma yana haifar da barazana.

Ya bayyana cewa rikicin Najeriya ya kasu gida biyu:

🔺 1. Arewa maso gabas:

– Tsattsauran ra’ayi mai alaka da kungiyoyin ta’addanci na duniya.

🔺 2. Arewa maso yamma:

– Matsalar tattalin arziki:
fashin shanu, kidnap-na-kuɗi, sare itatuwa, illegal mining, da sauran haramtattun sana’o’i.

SGF Akume ya jaddada cewa labaran da ba su da tushe daga kasashen waje na iya janyo rikice-rikice masu tsanani idan ba a yi hattara ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button