Labarai

Mai magana da yawun APC na Kano ya zargi fadar shugaban kasa da yiwa Ganduje zagon kasa

Kano Focus ta ruwaito cewa Kakakin jam’iyyar APC na Kano, ya zargi fadar shugaban kasa da yiwa Ganduje a kano, Alhaji Ahmad Aruwa, ya zarge shi da yin zagon kasa ga shugaban riko na jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje da kuma hada baki.

Mista Aruwa ya bayyana wadannan ikirari ne a cikin wani dan takaitaccen faifan bidiyo da ya fitar a Kano yana yawo a kafafen sada zumunta inda ya zargi wasu dakaru da ke fadar shugaban kasa da ke yunkurin tsige tsohon Gwamnan Jihar Kano a matsayin shugaban jam’iyar Apc na kasa.

Ya kuma tabbatar da sanin mutanen da ke da hannu wajen yin zagon kasa ga kokarin Gwamna Ganduje, da nufin karya alakarsa da Shugaban kasa.

Ya yi gargadin yiwuwar samun gagarumin rigingimun siyasa idan har wasu ‘yan jam’iyyar APC suka kuskura su ka yi adawa da Ganduje a Najeriya kasancewar yana daya daga cikin ginshikan nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023.

Za mu fuskanci duk wanda ke cikin APC da ya kuskura ya kalubalanci Ganduje, ba tare da la’akari da matsayinsa ko tasirin siyasarsa ba.”

Mista Aruwa ya kuma soki Tinubu da yin watsi da goyon bayan da aka ba shi a Kano lokacin da wasu suka ki shi.

Ya lura cewa babu kowa a Kano, jihar da ta fi yawan masu kada kuri’a da zai goyi bayan manufar Tinubu, domin Ganduje ne kadai ya tsara nasararsa a jihar. Don haka, ba za su amince da duk wani zagon kasa a Villa ba.

“Na yi alkawari da gaske cewa idan wani zai fuskanci Ganduje a cikin jam’iyyar APC, to babu makawa zai haifar da rikicin siyasa wanda a shirye muke mu yi yaki da shi.”

“Ba tare da la’akari da sunan mutum ba, muna sane da makirci da tuggu da wasu ‘yan jam’iyyar APC suka shirya a fadar Villa.

Wata majiya mai tushe daga fadar shugaban kasa da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa rigimar ta Ganduje ta faro ne a lokacin da aka umarce shi da ya ja hankalin gwamnan Kano Abba Yusuf da uban siyasarsa Rabiu Kwankwaso kan su yi watsi da jam’iyyar ta (NNPP) su koma jam’iyyar APC mai mulki.

An ruwaito cewa batun ya saba wa sharuddan da aka bai wa Gwamna Ganduje, ya isa Kano inda ya jagoranci taron masu ruwa da tsaki inda ya yi wa Kwankwaso da Gwamnan Kano ba’a da shagube lamarin da ya kawo cikas wajen tattaunawa da tawagar Kwankwaso.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button