Labarai

Makarantar Horon Aikin Soja ta NDA kaduna na kokarin kafa wani Sabon ta’addanci a Arewa…

~Makarantar ta bawa Sojoji Horon yaki da ta’addanci na tsawon Shekaru kuma a karshe sunyi masu korar Kare…

Ga Wani Labari mai ban takaici da ban Haushi tare da kawo barazana da rayukan al’umma Kuma labarin da yakamata Hukumomin tsaron Nageriya harzuwa Kan Gwamnatin tarayya su dauki matakin gaggawa Kan Al’amarin mai cike da Zalunci Wanda ya faru a Makarantar Tsaro ta Najeriya, wato Nigerian Defense Academy (NDA) dake Kaduna matasa ‘yan Nageriya masu Cikakken ‘yanci masu kishin Kare martar kasar Nageriya sunyi anfani da kuruciyarsu sun shiga makarantar tsaron Nageriya domin bayar da tasu gudunmawar musaman a wannan lokacin da muke Ciki na fama da matsalar tsaro a Arewacin Nageriya sun Sami nasarar shiga makarantar tare da kwashe shekaru masu tarin yawa suna karbar horon aikin soja a fanni da dama haka kawai Rana daya makarantar ta bayar da sanarwar cewa ta Kori matasan har mutun 53
wadanda akasarinsu ke gaf da fita a Makarantar daga cikinsu akwai jami’ai mutun Tara 9. Wanda tuni sun mallaki matakin samun POP dinsu kuma an basu lambar shedar Digirin girmamawa a hukumance a wani biki da mataimakin shugaban kasa Frof Yemi Osinbajo ya halarta a ranar 3 ga Oktoba, na 2019.

M.I Daura Matashin ne Yana daya daga Cikin wa’yanda suka samu horo a fanni kala kala na fasahar yaki da ta’addanci na tsawon shekaru hudu 4 a Makarantar ta NDA ya Kuma Yi shekaru shida a Makarantar Horon Aikin Soja dake Zaria (Nigerian Military School Zaria) Wanda shekaru goma kenan Yana karatun aikin Soja, M.I Daura ya bayyana dalilin dayasa akayi masu wannan aika aikar inda yake cewa Wanda ya haifar Mana da matsalarmu shine LT COL DODO domin bukatar kansa a wata Ranar juma’a jum kadan bayan gabatar da atisayen kammala bitarmu (passing out parede Reharsal) kawai sai shi DODON ya turo mana ofisa Mai suna MAJOR OTALU da wata takarda dauke da jerin sunayenmu (Name Iist) da nufin yazo ya daukemu domin Zuwa azabtar damu Haka kawai na tsawon kwana guda ana gana mana azaba shi wanna Ofisa din ya hanamu muje ko Ina Koda kuwa Zuwa canja kayanmu a daki, ya sake cewa damu muyi gaggawar cire Bel dinmu mu daure tare da hulunanmu Kuma mu bawa wasu abokan karatunmu domin za’a sake bamu wata sabuwar azabtarwar ya hanamu muci abinci yaci gaba da bamu azaba Yana Kuma daukar hotonmu Yana turawa shi LT COL DODO domin ya tabbatar da cewa aikin Daya sashi Yana tafiya daidai ba tare da wata matsala ba, Ba’a
tsaya da bamu azabar ba sai da muka sake kwana Zuwa karfe 8 na safe Wanda a daidai Wannan lokacin ‘yan uwan karatunmu sun kammala atisayen su, Bayan kammala komai da komai bisa ka’idojin Makarantar Babu wani laifi da muka aikata Wanda ya sabawa Makarantar Amma shi DODO yaki daina Dora Mana laifin cewa munyi Rashin Samun matakin P.O.P

To meyasa za’a sake dawo da binciken salsalar Baya (Dossier Review) wanda Kuma a bayyane yake kowa ya sani a dokar kundin tsarin Makarantar ba’ayima mutun Review sau biyu a shekara daya to ni meyasa akayi mun? Kuma ance an koreni bayan kwashe shekaru Ina koyon hikima da fasar yaki kawai sai ace an koreni wanne laifi na aikata kawai don Naki Aminta da bukatar da LT COL DODO Ya zomin da ita kan ‘aikata manya manyan miyagun laifuka? Hakika wannan ba adalci aciki Kuma BAZAMU aminta ba zamu bi hakkinmu ta hanyoyin da suka dace domin dawo da kimarmu..

M I. daura Ya kammala karatunsa da shedar Digirin girma Kuma Ya Samu takardar shedar kammala karatunsa Kuma shine na lamba 88 Cikin jerin wa’yanda Suka kammala karatun passing Out,

Yanzu Haka Kuma Bayan M.I daura Akwai mutun Tara 9 duk kansu suna da matakin P.OP da COL DODO ya kora Wanda tuni dai bincike ya tabbatar Mana da cewa domin bukatar kansa ne kawai ya aikata Hakan domin mun tabbatar da Haka a lokacin da Makarantar suka gabata a gaban Majalisar wakilan Nageriya domin fara bincike Kan faruwar Al’amarin.

Wasu na ganin korar jami’ai irin wannan ta kwararru a fagen yaki ba karamin kalubale bane ga tsaron Kasa musamman a wannan hali da muke Ciki Na Rashin tsaro..

Wannan kadan ne muka tsakuro maku Kan labarin Amma muna Mai tabbatar maku cewa zamu cigaba da bibiyar wannan labarin domin tabbatar da adalci ga maishi…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button