Masu garkuwa da mutane sun bukaci N70m su sako tsohon mataimakin gwamnan Nasarawa

LAFIA – Kasa da sa’o’i 24 da sace tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Farfesa Onje Gye Wado, masu garkuwa da mutane sun nemi kudin fansa naira miliyan 70 domin a sake shi.
Majiyar dangi wacce ke sa ido kan abubuwan da ke faruwa. Ya shaida wa wakilinmu cewa masu garkuwa da mutanen sun yi kira a karon farko tun bayan da aka sace Farfesa Onje Gye Wado inda suka bukaci a biya su Naira miliyan 70 kudin fansa domin a sako wadanda aka sace.
Idan ba a manta ba wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba ne suka yi garkuwa da Farfesa Onje Gye-Wado a daren ranar Alhamis a kauyen Rinz na karamar hukumar Wamba.
Majiyar ta ce “masu garkuwa da mutanen suna tuntubar iyalan Farfesa kuma sun bukaci a biya su Naira miliyan 70, yayin da iyalan kuma suka yi tayin naira miliyan biyu.
Bayanan da wakilinmu ya samu ya nuna cewa ‘yan uwa na rokon wadanda suka yi garkuwa da shi da su karbi miliyan biyu saboda ba za su iya tara abin da ya wuce miliyan biyu ba saboda hutun da gwamnatin tarayya ta ayyana na bikin Easter.
“Yau Juma’a, har zuwa Litinin, hutu ne na jama’a, babu inda za mu iya samun kudi kuma muna son shi (Prof), ya dawo da rai,” in ji majiyar.
