Labarai

Matsalar Tsaro a jihar Kaduna Yakamata Jama’a su taimaki Gwamnati da bayanan sirri ~Sanata Uba Sani

A Lokacin gabatar da sakonsa na ta’aziya ga Harin ta’addancin Unguwar Rigasa Sanata Uba Sani Mai wakiltar kaduna ta tsakiya Yace ina cike da bakin ciki da samun labarin Rasuwar Mal. Abdulazeez Adebayo, wanda tsohon Kwamishina ne na alakar gwamnatoci a jihar Kaduna yakasance Mai kaifin basira da kuma mai da himmar gaske, ya sanya kwarewarsa da tasirin sa wajen yiwa jam’iyyar APC aiki a jihar Kaduna. Gudummawar sa ba ta da iyakar lissafi. Ina mika ta’aziyyata ga danginsa, abokansa, abokan aikinsa Inji Sanatan.

Sanatan ya Kara da cewa dukda Ina cikin radadin rashinsa Mal. Abdulazeez Adebayo, an Kuma ba ni wani labarin rasuwar mai raɗaɗi na wani saurayi Dan gwagwarmaya, Mal. Rabiu Auwal. Wanda harin ‘yan fashi a Rigasa, Kaduna ya halaka shi, Ina ta’aziya ga danginsa. Ina kuma yin addu’ar Allah Ya gaggauta samun sauki ga wadanda suka samu raunuka bisa faruwar wannan Al’amarin na Bakin Ciki.

Hakika dubun barayin da masu satar mutane a jihar Kaduna ya kusa cika. Gwamnatin jihar Kaduna ta ninka kokarin ta na tabbatar da tsaron mutanen Rigasa da ma jihar Kaduna Baki daya. Koyaya yana buƙatar goyon bayan mutane a fagen tattara bayanan sirri. ‘Yan fashi da masu satar mutane basu kasance fatalwa ba dole Suna zaune a tsakiyarmu. Bari mu yi iya kokarinmu inya so saimu bar sauran ga Gwamnati da hukumomin tsaro…

Da fatan Allah ya gafarta kurakuran wadanda suka rasu ya kuma ba su Aljanna. Ameen

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button