Muna da tabbacin yanzu sabon Shugaban sojojin Nageriya zai kawo karshen ta’addanci a Nageriya ~El rufa’i.


Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce babban hafsan sojin kasar, COAS, Manjo Janar Taoreed Lagbaja, zai kawar da ta’addanci da ‘yan fashi a kasar nan.
El-Rufai, wanda ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a karshen makon da ya gabata, ya ce Lagbaja na kan gaba ne daga gaba, inda ya kara da cewa ‘yan ta’addan Boko Haram, ‘yan bindiga, ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, da sauran masu aikata laifuka na tsoronsa.
Tsohon gwamnan wanda ya saka wani hoton bidiyo na sabon hafsan sojan kasar yana kira sojoji da su kakkabe duk wasu masu aikata laifuka tare da dakatar da kashe-kashen da ake yi a jihar Filato, ya ce Lagbaja ya taba rike mukamin babban kwamandan rundunar, GOC, a lokacin gwamnatinsa na gwamnan Kaduna.
Ya ce: “Sabon nau’in hafsan hafsoshin soji wanda ba tare da shakka ba zai kawar da ta’addanci, ‘yan fashi, barna da tsageru a Najeriya.

