Sanusi Ya Yi Ganawar Sirri Da Tinubu

Ganawar na zuwa ne mako guda bayan da shugaban kasar ya dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin kasa na CBN.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaban kasa, Bola Tinubu, ya yi wata ganawar sirri da Sarkin Kano na 14 kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Sanusi Lamido Sanusi, a fadar gwamnati.
;
Ziyarar ta Sanusi, wadda ita ce ta farko tun bayan da shugaban kasar ya hau karagar mulki, na zuwa ne mako guda bayan da shugaban kasar ya dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan CBN.
;
Kawo yanzu dai ba a fayyace ajandar taron ba.
Sanusi ya rike mukamin shugaban CBN daga watan Yunin 2009 zuwa watan Yunin 2014 lokacin da Emefiele ya karbi mulki daga hannun sa.
A ranar Juma’a ne shugaban kasar ya dakatar da Emefiele a matsayin shugaban babban bankin sannan kuma ya umurci mataimakin gwamnan a aiyuka na bankin, Folashodun Shonubi, ya koma ofishinsa a matsayin mukaddashi.
A ranar Asabar din da ta gabata ne hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta tabbatar da cewa Emefiele yana hannun ta.
A ranar Laraba, babban bankin ya haɗa dukkan sassan na kasuwar forex yana ruguza duk tagogin da suka gabata zuwa ɗaya.

