Shehu Sani Ya Caccaki Gwamna Masari Kan Kudurinsa Na Rabawa ‘Yan Ta’adda Gonaki Da Rumfunan Kasuwa A Jihar.
Shehu Sani, tsohon dan majalisar dattijai a majalisar dokoki ta 8 ya soki dabarun da gwamnatin jihar Katsina ke da niyyar amfani da su don magance matsalolin rashin tsaro a jihar.
A cewarsa, shawarar da gwamnatin jihar Katsina za ta bayar ga ‘yan fashin (wadanda ke shirye su mika wuya) filayen noma, rumfunan kasuwa da gidaje, zai sa ta’addanci ya zama mai daɗi da riba.
Ya kuma kara da cewa aikin zai kara wa wadannan ‘yan fashi gwiwa, tare da karfafa gwiwar wasu su dauki makamai.
Kuma idan haka ta kasance, kalubalen rashin tsaro a arewa maso yamma da arewa ta tsakiya zai ta’azzara.
Ya rubuta kamar haka: “Kudirin da Gwamnatin Katsina ta gabatar na bayar da gonaki ga ‘yan fashi da makami, da rumfunan kasuwanni da Gidaje ya zama abin birgewa da kuma ba da lada ga ta’addanci.
Hakan zai kara wa’ yan fashin gwiwa ne kawai, ya karfafa wasu su shiga kuma ci gaba da kara dagula lamarin a arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.
“Biyo bayan sakon tsohon sanatan, wani dan Najeriya da ya damu ya amsa kamar haka: “Wannan abin kyama ne. Kamar kai tsaye yake daukar nauyin ta’addanci da aikata laifuka. Ba za a iya yarda da shi ba!”
Mutane da yawa sun yi adawa da ra’ayin, inda wasu ke cewa ba dabara ba ce.


