Labarai
Sojojin Nageriya sun kashe ‘yan ta’addan Boko Haram mutun 33 a Borno.
Dakarun na Special Forces Brigade a jihar Borno sun fatattaki mayakan Boko Haram sun kashe 33 a Chikingudu, wani gari a karamar hukumar Marte ta jihar Borno.
PRNigeria ta tattaro cewa an kashe yan ta’addan ne a ranar Talata bayan sojoji sun fafata dasu a yayin artabun yayin fatattakar mutanen Missene, Hausari da Chikungudu daga Marte.
An rasa sojoji biyu yayin artabu da ‘yan ta’addan.
An gano cewa sojoji bakwai kuma sun samu raunuka yayin fada da maharan.
Sojoji sun kwato akalla bindigogi kirar AK-47 guda 25, bindigogin harba jirgin sama guda uku, manyan bindigogi guda uku, manyan motoci biyu na atomatik, AGL, da manyan motocin daukar bindiga guda biyu.

