Labarai

Tallafin Man Fetur: Gwamnan Juhar Edo ya kara mafi karancin albashi zuwa N40,000 tare da rage kwanaki aiki zuwa kwana uku a mako

Gwamnan Jihar Edo, Mista Godwin Obaseki, a ranar Talata ya sanar da rage kwanakin aiki ga ma’aikatan gwamnati zuwa kwana uku a mako domin magance wahalhalun da jama’a ke fuskanta a halin yanzu sakamakon cire tallafin man fetur.

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kan sa, Obaseki ya ce “A sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi, farashin man fetur ya karu ta fuskar kudi wanda ya kai ga tashin farashin kayayyaki da ayyuka da kuma tsadar rayuwa baki daya.

“Gwamnatin Jihar Edo tana sani akan radadin da al’ummarmu ke ji, kuma tana so ta tabbatar wa kowa da kowa cewa muna tare da su a wannan mawuyacin lokaci.

“Muna so mu tabbatar wa mutanenmu cewa za mu yi duk abin da za mu iya a kan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na cire tallafin mai don rage radadin da kuma magance matsalolin da mutanenmu ke fuskanta a halin yanzu saboda abubuwan da ke faruwa a yanzu.”

Gwamnan ya ci gaba da cewa gwamnatin sa ce ta kara mafi karancin albashin ma’aikata a jihar Edo daga N30,000 da aka amince da shi zuwa N40,000, wanda shi ne mafi girma a kasarnan a yau.

“Muna so mu tabbatar muku da cewa za mu ci gaba da biyan wannan kudi, yayin da muke fatan za mu kara karawa, idan aka samu karin kaso daga gwamnatin tarayya a jihar mu bisa la’akari da tanadin da ake sa ran za a samu ta hanyar cire tallafin man fetur.

“Mun san irin wahalhalun da wannan manufar ta haifar wanda ya kara tsadar sufuri, tare da yin gibi a albashin ma’aikata a Jihar. Don haka gwamnatin jihar Edo ta rage yawan kwanakin aiki da ma’aikatan gwamnati za su rika zuwa wuraren ayyukansu daga kwana biyar a mako zuwa kwana uku a mako har sai an sanar da su. Yanzu ma’aikata za su yi aiki daga gida kwana biyu kowane mako.

“Hakazalika, ga malamai da iyaye, za a rage yawan zirga-zirgar su zuwa makaranta yayin da gwamnati ke kokarin zurfafa shirin EdoBEST@Home don ƙirƙirar ƙarin azuzuwa, ta yadda za a rage tsadar zirga-zirgar kan iyaye, malamai da ɗalibai. Edo SUBEB za ta ba da cikakkun bayanai kan wannan shiri a cikin kwanaki masu zuwa.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button