Tinubu ya nemi taimakon Tarayyar Turai EU don magance rashin tsaro da talauci a Najeriya

Shugaba Bola Tinubu ya bukaci Tarayyar Turai da ta tallafa wa Najeriya wajen magance matsalolin rashin tsaro da talauci a kasar da kuma Afirka.
A cikin wata sanarwa da Abiodun Oladunjoye, mai magana da yawun sa ya fitar, Tinubu yayi magana a ranar Laraba yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da Charles Michel, shugaban majalisar Turai.
Tinubu ya bukaci kungiyar EU da ta yi la’akari da wuraren da ake fama da matsalar tsaro musamman a kasar da ke makwabtaka da tafkin Chadi da sauran yankunan bakin teku.
Sanarwar ta kara da cewa, “Majalisar Turai ita ce cibiyar EU wacce ke bayyana alkiblar siyasa gaba daya da fifikon Tarayyar Turai.”
“A cewar shugaba Tinubu, Najeriya da daukacin Afirka za su bukaci taimako da hadin gwiwar abokanta da abokan ci gaba kamar EU don magance tsananin talauci a nahiyar.
“Yayin da yake neman Tarayyar Turai ta duba takamaiman yankunan da ke fuskantar kalubalen tsaro kamar tafkin Chadi da yankunan bakin teku, shugaban na Najeriya ya yi alkawarin ci gaba da tuntubar kungiyar Tarayyar Turai da sauran kasashe mambobin kungiyar.”
Ya ce gwamnatinsa za ta ba da fifiko kan matsalar talauci da rashin tsaro, inda ya ce zai yi duk abin da ya dace don tunkarar kalubalen.
A nasa bangaren, Michel ya taya shugaban kasar murnar nasarar da ya samu a zaben, ya kuma bukace shi da ya ci gaba da hada kai da kungiyar EU a dukkan fannoni.
Tinubu ya hau kujerar ne bayan rantsar da shi a matsayin shugaban Najeriya na 16 a ranar 29 ga watan Mayu.

