Labarai

Tinubu ya tafi kasar Faransa ne domin ya huta da kuma aikin Umara a Saudiyya – Kakakinsa

Tunde Rahman, mai taimaka wa Bola Tinubu, zababben shugaban kasa kan harkokin yada labarai, ya ce shugaban nasa ya tafi Turai.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Rahman ya ce Tinubu ya bar Legas ne a daren Talata zuwa birnin Paris domin hutawa da kuma shirye-shiryen aikin Umara a Saudiyya da kuma azumin watan Ramadan da za a fara ranar Alhamis.

Kakakin ya ce, zababben shugaban kuma zai yi amfani da damar, yayin da yake kasar waje, wajen tsara shirin karbar mulki.

“Zababben shugaban kasar ya yanke shawarar yin hutu ne bayan yakin neman zabe da kuma lokacin zabe domin ya huta a Paris da Landan, yana shirye-shiryen zuwa Saudiyya don yin Umrah da kuma Azumin Ramadan da zai fara ranar Alhamis,” in ji Rahman.

“Yayin da zai tafi, kuma zababben shugaban zai yi amfani da damar wajen tsara shirin karbar mulki.

“Ana sa ran zai dawo kasar nan ba da jimawa ba.

“Muna umurtar kafafen yada labarai da su daina buga jita-jita da ikirarin da ba su da tushe sannan kuma su rika neman karin haske daga ofishinmu.”

Ci gaban da aka samu zai haifar da cece-ku-ce kan inda zababbun shugaban kasar yake.

Tinubu dai bai fito fili ba na wasu kwanaki, lamarin da ya kara rura wutar rade-radin cewa watakila ba ya kasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button