Labarai
Tsohon Shugaban Nageriya Buhari ya Taya ‘yan Nageriya murnar ranar samun ‘yan cin Kai ya Kuma ce tabbas Dimokuradiyya zata cigaba samun karfi a Nageriya.


Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da gaisuwar ban girma ga shugaban kasa Bola Tinubu da al’ummar Najeriya bisa bukin cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai.
Buhari, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya fitar ranar Asabar, ya bayyana cewa: “A yayin bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kai, ina mika sakon gaisuwata ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da al’ummar Najeriya.
“Tsawon shekaru 63, Najeriya na ci gaba da zaburar da sauran kasashen nahiyar kwarin gwiwa da kirkire-kirkire da bambancin al’ummarta, kuma a yanzu, tsawon lokacin mulkin dimokradiyya. Ina da kwarin gwiwa cewa dimokuradiyya a matsayin tsarin gwamnati za ta ci gaba da samun karfi kowace shekara a cikin al’ummarmu.
“Happy Anniversary”