Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Wani Sabon Harin Zamfara

Sojoji sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu, alburusai, shanu, awaki da jakuna da ba a tantance adadinsu ba.

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyukan Sakiddar Magaji da Janbako dake karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara, inda suka kashe mutane akalla 10.

Wasu majiyoyi daga al’ummar Janbako sun tabbatar wa gidan talabijin na Channels afkuwar lamarin a ranar Lahadi, inda suka ce wasu da dama sun samu raunuka daban-daban.

Dangane da harin na baya-bayan nan, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa al’umomin biyu a karamar hukumar Maradun.

Ya kuma bayyana harin a matsayin na dabbanci da kuma cin zarafi ga mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, ya kara da cewa gwamnatinsa ba za ta nade hannunta ba tare da barin masu aikata miyagun laifuka su kaddamar da ta’addanci ba tare da wani tasiri ba.

“Wannan abin takaicin ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatinsa ke aiki tukuru wajen tsara dabarun yadda za a kawo karshen matsalar tsaro da ta dade a jihar,” in ji Lawal a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Mustapha Jafaru ya fitar.

“An bayar da umarni ga shugabannin hukumomin tsaro a jihar nan da su gaggauta tura karin jami’an tsaro ga al’ummomin da abin ya shafa domin dakile ci gaba da lalata rayuka da dukiyoyi a yankin.”

Da yake jajantawa iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu, gwamnan ya jajanta wa mutanen da suka samu raunuka a harin tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu.

Hakazalika, dakarun Operation Hadarin Daji sun kashe ‘yan ta’adda biyar da suka kai hare-hare a kan al’umomin.

Wata majiya mai karfi a jihar ta shaidawa gidan talabijin na Channels cewa sojojin da aka tura a Forward Operating Base Bakura a lokacin da suke sintiri sun samu sahihin bayanai na harin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Rogoji dake karamar hukumar Bakura da kauyen Sakiddar Magaji dake gundumar Janbako a karamar hukumar Maradun.

“Da isar su kauyen, ‘yan fashin sun gudu bayan da suka ga sojoji suna ci gaba, a sakamakon haka, sojoji sun ci gaba da bibiyar ‘yan bindigar da mumunar gobara kuma a cikin haka, an kashe ‘yan bindiga biyar,” in ji majiyar.

Sojojin sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu, alburusai, shanu, awaki da jakuna da ba a tantance adadinsu ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button