Labarai

Yan bindiga sun sace yara 80 a Zamfara

Har yanzu dai wadanda suka yi garkuwa da su ba su kai ga isa wurin iyayen ba domin su gabatar da wata bukata.

Yaran suna tsakanin shekaru 12 zuwa 17, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Wasu iyayen yaran da aka sace da suka zanta da kafar yada labarai ta Burtaniya sun ce wadanda aka sace suna cikin daji suna diban itace da karfe 8:00 na safe, inda maharan suka tare su suka tafi da su cikin dajin.

Al’amuran ‘yan bindiga sun ki tsayawa a Zamfara duk da yunkurin gwamnati na dakile ayyukan ta’addanci. An yi garkuwa da daruruwan ‘yan makaranta wasu kuma an sake su bayan an biya su kudin fansa.

Har yanzu wadanda suka yi garkuwa da su ba su kai ga tuntubar iyayen ba domin gabatar da wata bukata har zuwa lokacin da BBC ta bayar da rahoton sace su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button