Labarai

‘Yan sanda a jihar Bauchi sun bayyana cewa suna neman Yakubu Shehu dan majalisar wakilai ruwa a jallo bisa zargin kisan kai, tare bayar da tukwicin miliyan daya ga duk wanda yasan inda yake

Rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta bayyana cewa tana neman Yakubu Shehu dan majalisar wakilai bisa zargin kisan kai.

NAN ta ruwaito cewa ‘yan sandan sun kuma dora masa tukuicin N1m.

Dan majalisar dai yana wakiltar mazabar tarayya ta Bauchi ne a majalisar wakilai ta kasa.

Ana neman Yakubu ne kan wani shari’a na hada baki, da haddasa mummunar illa, tada hankalin jama’a, da kuma kisan gilla.

Ahmed Wakil, kakakin rundunar ‘yan sandan Bauchi, ya fitar da wata sanarwa ta musamman ta ‘yan sanda inda ta bayyana cewa ana neman sa a ranar Talata.

“’Yan sanda suna neman duk wanda ke da sahihin bayanin da zai kai ga kama shi domin yi masa tambayoyi da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zargin aikata laifuka,” in ji sanarwar.

“Duk wanda ke da bayanin da zai taimaka wajen kama shi to ya tuntubi 08151849417 ko kuma ya kai rahoto a ofishin ‘yan sanda mafi kusa.”

Rundunar ‘yan sandan ta yi kira ga duk wanda ke da bayanai masu amfani game da inda yake da ya tuntubi hukuma.

An zabi dan majalisar a matsayin dan majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar PRP.

Ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a 2022 amma daga baya ya karbi tikitin takarar sanata a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button