Labarai
‘Yan Sanda Sun Gano Bindigogi Kirar AK 47 Da Aka Yi Amfani Da Su Yayin Satar Bankin Ondo a Jihar Oyo.

Rundunar ‘yan sanda a jahar Ondo ta ce ta kwato wasu bindigogi kirar AK 47 guda hudu da aka yi amfani da su wajen sata a wani banki a yankin Ile Oluji na jihar Ondo.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jahar Ondo, Tee-Leo Ikoro, ya bayyana cewa, an maido da bindigan ne bayan wani mummunan fashi da ya faru a jihar Oyo.
Ya ce, “An gano bindigogin ne bayan da wasu ‘yan fashi dauke da makamai suka yi watsi da su a wani samamen da suka yi a kan yan fashi da makami a jihar Oyo.
Ikoro ya yi kira ga mutanen jahar da su taimaka wa ‘yan sanda da wasu bayanai masu amfani wadanda za su taimaka wajen dakile duk wani nau’in aikata laifi a jahar.
Ahmed T. Adam Bagas


