Yanzu haka mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya sauka a Amurka domin hakartar Taron Abinci na duniya.

Mataimakin shugaban kasar Kashim Shettima ya isa kasar Amurka domin halartar Taron Abinci na duniya da za a gudanar a jihar Iowa.
Taron wanda Norman E. Borlaug Tattaunawar Duniya ta shirya zai fara a ranar Talata, 24 ga Oktoba, 2023.
Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa a ranar Lahadin da ta gabata ta hannun mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa (Ofishin Mataimakin Shugaban kasa), Mister Stanley Nkwocha, yana mai cewa mataimakin shugaban kasa wanda shi ne babban bako a wajen taron shi ma zai gabatar da jawabi.
Zai kuma gudanar da manyan tarurruka tare da masana’antun, masu zuba jari da manyan jami’an gwamnati a wasu jihohin Amurka.
Shettima zai yi amfani da wannan dandali wajen yin magana da iyawa da baiwar da ake samu a fannin noma a Najeriya, da jan hankalin masu zuba jari da kuma matsa kaimi wajen cimma manufofin shugaba Bola Tinubu da kuma shirye-shirye na bangaren abinci na Najeriya.
Manyan shugabannin Afirka da a baya suka yi amfani da taron wajen zayyana tallafin noma da wadatar abinci a Afirka sun hada da Marigayi tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya kuma wanda ya kafa kungiyar AGRA, Kofi Annan, da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo, da Shugaban kasa Felix Tshishiked da Joaquim Chissano, da kuma Shugaban AfDB, Akinwunmi Adeshina da sauransu.