Labarai
Yanzu-yanzu: Buhari ya nemi amincewar majalisar dattawa kan fitar da $556m, £98m, domin ya biya bashin N226bn

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattawa da ta amince da bukatar biyan wasu makudan kudade a matsayin basussuka.
Kudaden da suka hada da dala $566,754,584, fam 98,526,012 da kuma Naira biliyan 226 — da ake bin gwamnatin tarayya.
Ahmed Lawan, shugaban majalisar dattawa, ya karanta wasikar bukatar shugaban kasa a wani zama na yau Laraba.
Karin bayani zai zo daga baya..
