Rahotanni

Yarabawa Sun Kawo Karshen Ruga Na Fulani Yanzu Kuma Sun Kawo Karshen SARS, Ku Kunata Biyayya Ga Danku Yana Mulki Amma Kun Kasa Maganin Matsalarku, Jerry Samuel Ga ‘Yan Arewa.

Arewa An Sake Nuna Muku Yiwa Mai Kuntata Maka Biyayya Tare Da Mika Wuya Don Zama Bawan Jahilci Ba Shine Mafita Ba~In Ji Jerry Samuel.

A kasar yarabawa ake yin aikin kuma sune da mataimakin shugaban kasa har da kakakin majalisar wakilai.

Duk da haka sune ke kan gaba wajen nemawa Kansu mafita in wani bangare na gwamnati na takura musu.

Sun kawo karshen #Ruga na Fulani makiyaya, kuma yau sun kawo karshen #SARS, ku kuma ba dai mulkin kukeso fiye da cigaban yankin Ku ba,?

Ga ku ga mulkin, danku yana yi, muje zuwa amma kusani( heroes worshippers) masu bautawa shugabanni musamman masu kuntata musu ba zasu taba fita daga kunci ba.

Daga Kabiru Ado Muhd.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button