Za’a Hukunta Dukkan Masu Amfani Da Haramtattun Mitoci, Cewar Ministan Sadarwa. Dr Pantami
Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da sayowa da tura tsarin sanya ido na zamani don gano haramtattun mitocin hanyoyi a kudu maso gabas kan kudi N653, 886,584.
Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Dijital, Dakta Isa Ali Pantami ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar Shugaban kasa a karshen taron mako-mako na FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Fadar Aso Rock Villa, Abuja.
Ministan ya ce bincike ya nuna yadda ake amfani da mitoci ba bisa ka’ida ba, a kasar ya zama yana da yawa, ya kara da cewa daga cikin mitoci 320 da aka gano, 106 basa bisa doka ba.
Amma duk da haka, ya ce bisa shawarar da Babban Mai Shari’a na Kasa da Ministan Shari’a suka bayar, za a hukunta duk Wanda aka samu da mitocin ba bisa ka’ida ba. Daga Comr Haidar Hasheem Kano


