Zamanin Zaman Banza Da Rashin Cika AlkawurraSun Wuce, Muna Bukatar Mu Gina Sabuwar Najeriya Cikin Gaggawa, In Ji Atiku Abubakar.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya roki ‘yan Najeriya da kada su yanke kauna duk da kalubalen da ya addabi kasar.
Atiku a wata sanarwa ya kuma ce makomar Najeriya ta dogara ne da jajircewar masu ruwa da tsaki kan makoma daya.
“Wataƙila mun rasa damarmakinmu da yawa, don sake saita tunaninmu na ci gaba, kamar mutane masu ci gaba, amma wannan bikin na shekaru 60 na rayuwar al’ummarmu yana bukatar tunani.
“Domin Najeriya ta yi wa miliyoyin jama’arta aiki, kuma za a dauke ta a matsayin babbar kasa a duniya a nan gaba, dole ne mu fito da wani tsari na ci gaba da zai sanya matasanmu su kasance a cikin shiri.
“Zamanin zaman banza, da rashin cika alkawura sun wuce!
Muna bukatar mu gina sabuwar Najeriya cikin gaggawa, inda kowane irin buri namu zai kasance, kuma za a iya bawa matasanmu dama ba tare da fargabar da ta saba da mu ba.
“Ina kuma kira ga wadanda suka dauki makami don yakar Najeriya da su sake tunani.
Duk da irin kalubalen da muke fuskanta a Najeriya, na bambance bambance, walau na addini, na kabilanci ko na siyasa, ta’addanci, tashin hankali da rarrabuwar kawuna da sauransu.

