Cire tallafin man fetur bai haifar da komai ba sai kara ta’azzara matsalar man fetur – NANS ga Tinubu

Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta bayyana cewa cire tallafin man fetur da gwamnatin Bola Tinubu tayi bai haifar da komai ba ba illa kara tabarbarewar matsalar man fetur a kasarnan.
Kungiyar daliban ta ce tsarin cire tallafin ya jawo wa ‘yan Najeriya wahalhalun da ba a taba gani ba tare da haifar da karancin mai a maimakon samar musu da mai.
Don haka NANS ta yi kira ga Tinubu da NNPC da su nemo bakin zaren warware matsalar mai a kasar nan.
Kungiyar daliban ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da magatakardan majalisar dattawa ta kasa NANS, Abdul-Yekinn Odunayo, ya fitar a Abeokuta ranar Asabar.
“NANS ta damu matuka game da tsadar man fetur da kuma karancin man fetur da ake fama da shi a kasarmu.
“Wannan rikicin ya ci gaba da wanzuwa duk da cire tallafin man fetur wanda ya jawo wa ‘yan Najeriya wahalhalun da ba a taba gani ba.
“Wannan rikicin ba wai yana gurgunta tattalin arzikin kasa kadai ba, har ma yana yin tasiri sosai ga walwala da neman ilimi na dalibai a fadin kasar nan.
“’Yan Najeriya na fama da wahalhalun da ba a taba ganin irin su ba, kuma suna shiga cikin wahala kafin su iya sayen mai.
“Layi ya zama ruwan dare a gidajen mai a fadin kasar nan duk da alkawarin da shugaba Bola Tinubu ya yi na cewa layin man fetur zai bace a kasar bayan cire tallafin, amma abin ba haka yake ba.
“Tsarin farashin man fetur ya haifar da tashin gwauron zabi na sufuri, ya haifar da tashin gwauron zabi na kayan masarufi da ayyuka. Ana ba da ƙarin farashin sufuri da samar da kayayyaki ga masu amfani da shi, wanda ke ta’azzara tsadar rayuwa.
“Abin takaici ne cewa, shekara daya bayan cire tallafin man fetur ya kara ta’azzara kuma ga dukkan alamu kasar na tafiya cikin la’ana.
“Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa don magance wannan matsala kafin a tura ‘yan Najeriya bango,” in ji Odunayo.

