Uncategorized
Akwai Yiyuwar Karuwar Rikici Da Yunwa A Yakin Arewa Maso Gabas, Inji Majalisar Dinkin Duniya.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Majalisar dinkin Duniya ta bayyana cewa muddin ba’a dauki wani mataki ba to za’a ga karuwar tashe-tashen hakula da kuma yunwa a yankin Arewa maso gabas.
Wakilin majalisar, Edward Kallon a wani zama da aka yi kan rikicin na Arewa maso gabas da ya samu halartar gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum da Ministar kula da jinkai, Ss’adiya Umar Farouk ne ya bayyana haka.
Yace akwai kalla mutane sama da Miliyan 10 da lamarin ya shafa wanda ke bukatar tallafi. Yace kuma idan ba’a dauki mataki ba lamarin zai kazance.
