Uncategorized

Maryam Shetty Ta Taya Dr. Mariya Mahmud Murna..

Jim kadan bayan cire sunanta daga jerin sunayen ministoci da fadar Shugaban Kasa tayi tare da maye gurbinta da Dr. Mariya Mahmud, Dr. Maryam Shetty ta taya Mariya Mahmud murnar samun sunanta a cikin jerin sunayen ministocin da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai nada.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na twitter, Maryam Shetty ta ce tana taya Dr. Mariya Mahmud murna, sannan kuma ta mika sakon godiya ga Shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Dr. Maryam Shetty ta wallafa sakon nata ne da harshen turanci kamar haka: “I felicitate with Dr Mariya Mairiga Mahmud. I thank the leader of our party HE Abdullahi Ganduje for his fatherly disposition and democratic stance that set the stage for a free and transparent contestation devoid of institutional bias, favoritism, or imposition of any kind”.

Fassara: ” Ina taya Dr Mariya Mairiga Mahmud murna. Ina godiya ga jagoran jam’iyyar mu Abdullahi Ganduje bisa matsayinsa na uba ga tsarin dimokuradiyya wanda ya bude fagen yin takara cikin ‘yanci da gaskiya ba tare da nuna son kai, ko nuna son zuciya ba.

A ranar laraba ne shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya aike da jerin sunayen ministoci kashi na biyu ga majalissar dattawa, wanda a ciki akwai sunan Dr. Maryam Shetty, wanda da ya jawo cece-kuce a fadin kasar, musamman ma Arewacin kasar, yankin da Maryam din ta fito daga ciki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button