Da dumi’dumi: Kungiyar sanatocin Arewa sunce ba su aminta ayi anfani da karfin soja ba a Kasar Nijar.


Sanatocin Arewacin Tarayyar Najeriya sun yi Allah-wadai da juyin mulkin da aka yi a Nijar, tare da yin taka tsantsan kan amfani da karfin soji.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin kungiyar Sanatocin Arewa Sen. Kawu Sumaila.
Sen. Kawu Sumaila a cikin kalaman sa ya ce:
“Mu kungiyar Sanatocin Arewa ta Majalisar Dattawa ta 10 karkashin jagorancin Sen. Abdul Ahmad Ningi, mun lura da damuwa tare da yin tir da duk wani abin da bai dace ba a jamhuriyar Nijar, inda sojoji suka yi wa gwamnatin shugaba Mohammed Bazoum juyin mulki da karfin tsiya. ”
Sanatocin Arewa sun kuma yi la’akari da kokarin da shugabannin ECOWAS karkashin jagorancin mai girma shugaban kasarmu, Bola Ahmed Tinubu, suke yi, na magance al’amura a Jamhuriyar Nijar. Ya kamata a mai da hankali kan hanyoyin siyasa da diflomasiyya don maido da mulkin dimokradiyya a Jamhuriyar Nijar.
“Muna kuma barranta da yin amfani da karfin soji har sai an gaji da sauran hanyoyin kamar yadda aka ambata a sama, sakamakon zai zama hasarar rayukan da ba su ji ba ba su gani ba, wadanda ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum. Baya ga haka, kusan jihohi bakwai na Arewa da suka yi iyaka da jamhuriyar Nijar wato Sokoto, Kebbi, Katsina, Zamfara, Jigawa, Yobe da Borno za su fuskanci mummunar illa.”
“Muna sane da halin da ake ciki a Mali, Burkina Faso da Libya, wanda zai iya shafar jihohin Arewa bakwai, idan aka yi amfani da karfin soji. Akwai matukar tasiri ga kasarmu, idan aka yi amfani da karfin soja ba tare da gajiyar da dukkan hanyoyin diflomasiyya ba.”
“A matsayinmu na ‘yan dimokradiyya da wakilan jama’ar da muke nan ta hanyar kira ga abokan aikinmu da su lura da yadda ya kamata wajen yin amfani da sashe na 5 karamin sashe (4) (a) da (b) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 kamar yadda aka yi wa kwaskwarima.”
