Cikin Bidiyo: Gwanin sha’awa da burgewa, yadda matashiya Maryam MT take rangada zanen sunan Annabi Muhammadu (s.a.w) mai kayatarwa.
Cikin Bidiyo: Gwanin sha’awa da burgewa, yadda matashiya Maryam MT take rangada zanen sunan Annabi Muhammadu (s.a.w) mai kayatarwa.
Maryam Aminu Maikudi Tela shine cikakken sunan Matashiyar, haifagfiyar jihar Kaduna ce, ta kasance kwararriya ce a fannin zanen zayyanar sunayen Allah da ayoyin Alqur’ani mai girma.
Maryam dai Ɗaliba ce a Jami’ar Jihar Kaduna, tana karatunta ne a fannin ilimin hada magun-guna (permacy), amma duk da haka tana samun lokacin da take gudanar da sana’arta ta zayyana.
Maryam ta ce ” Na kasance ina yawan bibiyar masu zayyana ta kafofin sada zumunta ina ganin to yadda suke yi nima Ina kwatantawa, sannan kuma ina dakko bidiyoyi a yanar gizo ina kallon yadda ake yin zanen zayyana, a haka har na iya.”
Maryam ta ce mutane da yawa sun siya zanen zayyanar da ta wallafa, kuma har yanzu suna siya. Ta kara da cewa tana da burin bude shagon siyar da zayyana, kuma tana son ta bunkasa aikin zayyanar ta ya zamo ba iya Kaduna kadai ba, za a iya samun zayyanarta a ko ina…
Hotunan wasu daga cikin zanen da Maryam MT tayi.




