‘Yan bindiga sun sace Ɗalibai a makarantar sakandaren ‘yan mata ta gwamnati, da ke Jangebe a karamar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara.
An ce ‘yan bindigar sun isa makarantar da misalin karfe 1 na dare kuma suka loda’ yan matan a cikin bas.
‘Yan bindiga sun sace wasu’ yan mata ‘yan makaranta da ba a tantance adadinsu ba a makarantar sakandaren’ yan mata ta gwamnati, da ke Jangebe a karamar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara.
‘Yan bindigar wadanda ake zaton‘ yan fashi ne, sun far wa makarantar ne da safiyar Juma’a.
An ce ‘yan bindigar sun isa makarantar da misalin karfe 1 na dare kuma suka loda’ yan matan a cikin bas.
Wani mazaunin kauyen Kawaye mai suna Seidu Muhammadu wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga ya ce ‘ya’yansa mata, Mansura da Sakina na daga cikin wadanda aka sace.
“Ina kan hanyata ta zuwa Jangebe yanzu don ganin halin da kaina. An gaya min sun mamaye makarantar da misalin karfe 1 na dare,” in ji shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya shaida wa manema labarai cewa: “Ku ba ni wani lokaci, ba zan iya cewa komai yanzu ba.”
Lamarin na Zamfara na zuwa ne mako guda bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Kagara, Jihar Neja, inda suka yi awon gaba da daliban makaranta 47, malamai da ma’aikata, wadanda har yanzu ba a kubutar da su ba har zuwa ranar Juma’a.