Rahotanni

Makonni biyu bayan zabe, Shugaban Amurka Biden bai taya zababben shugaban kasa Tinubu murna ba

A watan Mayun da ya gabata, Mista Biden ya buga waya da zababben shugaban kasar Philippines Ferdinando Marcos Jr, domin taya shi murna. An buga cikakken bayanin kiran a shafin yanar gizon fadar White House.

Har yanzu dai wanda ya lashe zaben shugaban kasar Najeriya mai cike da takaddama, Bola Tinubu, bai samu sakon taya murna a hukumance daga shugaban kasar Amurka, Joe Biden ba, kamar yadda aka saba idan duk wata al’ummar da take ganin kawancen Amurka ke zabar sabon shugaban kasa.

Ganin cewa tsohon shugaban kasa, Barack Obama, ya taya Muhammadu Buhari murna a shekarar 2015, a daidai ranar da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben, shiru da Mista Biden ya yi makwanni biyu bayan nasarar da Mista Tinubu ya samu ya zama kamar ban mamaki.

A watan Mayun da ya gabata, Mista Biden ya kira zababben shugaban kasar Philippines na lokacin Ferdinando Marcos Jr ta wayar tarho domin taya shi murna. An buga cikakken bayanin kiran a shafin yanar gizon fadar White House.

A cikin irin wannan yanayi, shugaban na Amurka ya aike da sakon taya murna ga Luiz Inácio Lula da Silva, lokacin da ya fito ya lashe zaben shugaban kasa a Brazil a watan Oktoban 2022, wanda kuma aka buga a shafin yanar gizon fadar White House.

A maimakon haka, Ned Price, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka ne ya yi wa Mista Tinubu taya murna a madadin gwamnatin kasar waje yayin da kuma ya nuna cewa ‘yan Najeriya da dama sun ji takaicin yadda INEC ke gudanar da zaben.

Mista Price ya karfafa wa ’yan takarar da suka yi korafin kalubalantar nasarar da Tinubu ya samu a kotu a cikin sanarwar.

Maganar shiru da Mista Biden ya yi wa shugaban Najeriya mai jiran gado za a iya kallon shi a matsayin shakkunsa game da tsarin zaben da ya haifar da shi.

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce an karkata akalar zaben da kuma rashin gaskiya.

Hakazalika, wata cibiyar bincike ta Burtaniya, Chatham House, ta ce tursasawa, tashin hankali, da rashin bin ka’ida sun gurbata zaben shugaban kasa wanda ya baiwa Mista Tinubu na jam’iyyar All Progressives Congress nasara nasara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button