Sojojin Nigeria sun taba kashe makiyaya a jihar Nasarawa tunda aka ce za’ayi bincike Haryanzu babu Sakamakon ~Cewar Khalifa Sanusi Lamido

Tsohon sarkin kano Khalifa Muhammadu Sanusi Lamido Na II a wani faifan bidiyo dake yawo a kafafen sada zumintar zamani ya bayyana rashin Jin da’din sa tare da Allah wadai da kisan Gillar da sojojin Nageriya sukayi kan masu Taron Maulidi a Yankin Kauyen Biri Dake Karamar Hukumar Igabi ta jihar Kaduna wanda ake hasashen an kashe Al’umma sama da mutun Dari a Yankin.
A cikin Sakon sa ya yi ta’aziyya ga iyalan Al’ummar da abin ya shafa ya Kuma ta’aziyya ga Yan tijjaniyya da Gwamnatin Jihar Kaduna.
Ya kuma yi kira ga Al’ummar da su kwantar da Hankalin su domin ya samu labarin Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayarda Umarnin gudanar da bincike kan wannan al’amari, Tsohon sarkin ya yi kira da ayi bincike cikin gaggawa tars da fitar da Sakamakon binciken yace domin wannan ba shine farkon faruwar al’amarin ba a Arewacin Nageriya ya faru kan wasu makiyaya a iihar Nasarawa tida Gwamnati tace za’ayi bincike Haryanzu Babu Wani Sakamakon Daya fito.
