Zargi: Shugabar Hukumar da’ar ma’aikata ta tarayya Farida Dankaka ta sayar da guraben ayyuka a ma’aikatu da hukumomin Gwamnatin Tarayya kan kudi N750,000 zuwa Naira miliyan 7


“Masu neman aikin suna biyan Naira 750,000 zuwa Naira miliyan 7 ya dandanta da inda ake neman ayyukan.”
Kwamishinonin hukumar (FCC) sun zargi shugabar hukumar Farida Dankaka da “sayar da guraben ayyukan yi” a ma’aikatu da hukumomin tarayya (MDAs).
Kwamishinonin sun yi wannan zargin ne a lokacin da kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai ke binciken MDAs da jami’an tsaro da manyan makarantu kan badakalar ayyukan yi a Abuja.
Kwamishinonin FCC da suka yi zargin sun hada da Abdulrasaq Adeoye (Osun), James Dan’iya (Kwara), Abdulwasiu Bawan-Allah (Lagos), Moses Anaughe (Delta), Mamman Alakayi (Nasarawa), da dai sauransu.
Kwamishinonin sun kuma yi zargin cewa Madam Dankaka ta hada baki da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) don dakatar da wani koke da aka rubuta akanta kan badakalar aikin da kwamishinonin suka rubuta.
“Mun roki EFCC da ta bincike ta, amma abin takaicin mu ba a yi komai ba. Masu neman aikin suna biyan daga Naira 750,000, har Naira miliyan 7, ya danganta da MDAs inda ake neman ayyukan. Ana tura kudaden daga asusun daban-daban zuwa babban asusun bankin Access,” kamar yadda suka shaida wa kwamitin.
Kwamishinonin sun yi zargin cewa shugabar ta kan dauke danta daga wata hukuma mai riba zuwa wata.
A martanin da ta mayar dangane da yawaitar zarge-zargen, Madam Dankaka ta ce, “Idan ka yaki cin hanci da rashawa, cin hanci da rashawa zai yakeka.
Shugabar FCC ta kara da cewa, “Ban zo neman kudi ba sai don in yi wa kasata hidima. Abin da wasun su ke nema shi ne kudi. Kafin in zo nan, na yi kudi na. Wasu daga cikinsu suna da dalilansu na kai mini hari. Misali, kwamishinan Osun yana ofishina kullum. Abin da suke zargina da shi ba gaskiya ba ne.”
Madam Dankaka ta ce kafin ta shiga ofis a watan Yulin 2020, dukkan kwamishinonin suna “sayar da ayyukan yi,” ta kara da cewa kin shiga cikin badakalar ya sa suka fusata da ita.
A cewarta, alal misali, kwamishinan da ke wakiltar Osun ya sayi wata kadara kuma ya shaida wa mutumin cewa zai biya da guraben aiki.
A cewarta, hakan ya sanya ta aike wa MDAs cewa kada su girmama duk wata takarda daga kwamishinonin idan har ba su ga sa hannun ta ba.
Shugabar hukumar ta FCC ta ce ta ki amincewa da tayin nasu na sasantawa, inda ta kara da cewa ita ce za ta kasance mutum na karshe da zai sayar da ayyukan yi, kuma kwamishinonin na da hannu a yakin neman zabe a kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta.
Dangane da batun EFCC kuwa ta ce hukumar na son daukar ma’aikata ne kuma ta samu amincewar ta, inda ta ce babu wani lokaci da ta yi sulhu da su.
Shugaban kwamitin majalisar, Gagdi Yusuf, ya ce ‘yan majalisar ba za su shiga harkokin siyasar kowace hukuma ba.
“Za mu yi aikinmu, kuma za a yi adalci,” in ji Mista Gagdi.
Ya tambayi dalilin da ya sa za a yi zargin bacewar takardun da suka shafi ayyukan hukumar ta fuskar daukar aiki.
(NAN)
