Ministan Abuja Wike ya aminta a dagawa masallatai da coci coci Kafa Zuwa Wani lokacin a Abuja.

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya tsawaita wa’adin ‘ci gaba ko soke’ duk wani Abu Daya shafi kungiyoyin addini yana mai cewa za a ba su karin lokaci maimakon takardar sanarwar watanni uku da aka mika wa dukkanin cibiyoyin tun farko.
Wike a watan da ya gabata ya ba da sanarwa wa,adin watanni uku ga masu mallakar filaye 189 da ba a gina su ba don fara aiki ko ya soke lasisin mallaka.
Da yake jawabi a ranar Larabar da ta gabata lokacin da ya karbi bakuncin Hukumar Masallacin ta kasa, karkashin jagorancin Shugabanta, Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, Ministan ya ce Hukumar na kara wa kungiyoyin addini wa’adin ne saboda sun dogara ne da gudunmawar jama’a.
Tawagar ta je babban birnin tarayya FCTA ne domin neman karin haske kan yanayin filin ta na 63, inda aka umarce su da su dakatar da ci gaba a lokacin aikin hanyar Outer Southern Express.
Ya bayyana cewa, ya kamata a fara aiki a filin da ke daura da Cibiyar Yar’adua kafin a ba da sanarwar dakatar da aikin ga mahukuntan masallacin.
Hukumar ta kuma yi amfani da wannan dama wajen neman tallafi domin kammala aikin gyaran masallacin kasa na babban birnin tarayya Abuja, wanda hukumar raya babban birnin tarayya, FCDA ke aiwatarwa, kafin kaddamar da gwamnatin shugaba Tinubu.
Ya yi nuni da cewa, shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya amince da masallacin na kasa a matsayin abin tarihi na kasa, wanda ya kaddamar da shirin tara kudade domin gyara shi.
Sai dai kuma a kan fili mai lamba 99, mahaifin sarkin ya ce filin yana samun kulawar da ta dace domin majalisar ta samu amincewar tsarin ginin don fara ci gaba nan ba da jimawa ba.


